Gwamnan Neja Ya Kai Dauki Ga Daliban Makarantar Sojoji Da ‘Yan Ta’adda Suka Sare Su

FB IMG 15170546701806849 300x201 - Gwamnan Neja Ya Kai Dauki Ga Daliban Makarantar Sojoji Da 'Yan Ta'adda Suka Sare Su

Gwamnan Neja Ya Kai Dauki Ga Daliban Makarantar Sojoji Da ‘Yan Ta’adda Suka Sare Su

Tawagar gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello kenan akan hanyar su na zuwa Tungan Malam dake karamar hukumar Paikoro a lokacin da suka tsaya ceton ran wasu dalibai biyu na makarantar Army Day Secondary School Minna da wasu ‘yan sara-suka suka sassare su, a dai dai kofar kwalejin ilmi na Jihar Neja (COE Minna).
Gwamnan ya umarci likitocin sa su gaggauta duba daliban tare da daukarsu zuwa asibitin kwararru na Ibrahim Badamasi Babangida damin cigaba da duba lafiyar su, kazalika gwamnan ya umarci kwamishinan ‘yan sanda na Jihar ta Neja da ya gaggauta zakulo wadanda suka sassari daliban dan fuskantar hukunci.
Daga Comrade Zakari Y Adamu Kontagora

Updated: January 27, 2018 — 1:06 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Copyright © 2018 Leofirms.com - All rights reserved Leofirms.com is owned and managed by Kikiotolu Technologies Ltd.