Alamu na kara nuna cewa tsohon gwamnan jigawa wato Sule lamido da gaske yake game da takarar shugabancin kasa a 2019.
Arewa times ta samu wasu hotuna na motocin kamfen da gwamnan ya siyo, wadanda ke sintiri a jihar Jigawa da sauran wurare. Saidai abin tambaya shi ne anya Sule Lamido zai kai banten shi a zaben cikin gida na jam’iyyar PDP kuwa? Lokaci ne kawai zai tabbatar da haka
posted from Bloggeroid